ABNA24 : Majiyar gwamnatin kasar ta Sudan ta shaidawa jaridar cewa;An shirya cewa idan tawagar ta Isa za bude tattaunawa da jami’an kasar ta Sudan akan hanyoyin bunkasa alaka a tsakanin kasashen biyu.
Jaridar ta ce ga dukkanin alamu dambaruwar siyasar da Amurkan take ciki ne musabbanin dage ziyarar cikin gaggawa.
A ranar 23 ga watan Oktoba ne dai gwamnatin Sudan ta amince da kulla alaka da HKI, bayan da Amurka ta kafa mata sharadin cewa sai idan ta yi haka ne za a cire ta daga cikin jerin sunayen kasashe ‘yan tadda a wurin Amurka.
342/